Dangote ya tallafa kuma ya nuna sabbin kayayyakin kamfanin a kasuwar baje koli ta Kano

Date:

Daga Fa’iza Bala koki

 

Rukunin kamfanonin attajirin nan na Afirka Aliko Dangote ya karbi bakuncin mutane masu tarin yawa don ganin sabbin kayayyaki da ake nunawa na kamfanin a kasuwar baje koli ta Kano.

 

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka ziyarci rumfar kamfanin sun hada da manyan jami’an gwamnati, Sarakuna, masu zuba jari, malamai, da sauran manyan mutane.

 

Kamfanin wanda shi ne kan gaba wajen daukar nauyin bikin baje kolin kasuwanci karo na 43 , wanda cibiyar kasuwancin ma’adinai da noma ta Kano (KACCIMA) ke shirya wa.

 

Shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, shi ne uban cibiyar ta KACCIMA.

 

Mahalarta taron da suka yi cincirindo a rumfar kamfanin sun ce sun ji dadi da ingantattun kayayyakin da ake baje a wurin bikin na bana.

 

Talla

Cikin wadanda suka ziyarci rumfar kamfanin na Dangote har da sarakunan Gaya da takwaransa na Masarautar Bichi.

 

Yayin da yake gabatar da jawabinsa tun da farko, Alh. Aliko Dangote ya bayyana taken bikin, wanda ke ba da damar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ta hanyar AFCFTA don bunkasar tattalin arzikin Najeriya da ci gabanta,a matsayin abun da ya dace.

 

Mista Dangote ya samu wakilcin Daraktan shiyya na Dangote Cement Plc. Arewa maso yamma, Malam Aliyu Da’u Aliyu.

 

Ya yi nuni da cewa, AFCFTA za ta iya cewa ita ce makomar Afirka, inda ya kara da cewa DIL za ta taka muhimmiyar rawa a kasuwannin Afirka a matsayin kamfani na Afirka da duniya baki daya domin kara samun moriyar ciniki cikin ‘yanci a Nahiyar.

 

“Mun halartar bikin baje kolin na bana ne don ba da gudummawar kasonmu ga ci gaban tattalin arzikin jihar kano da Najeriya baki daya, Taken bikin na bana shi ne, ‘Ba da Damarar Fitar Da Kayayyakin ta hanyar AfCFTA domin Ci gaban Tattalin Arzikin Najeriya,” inji shi. .

 

Kamfanin tace danye mai na Dangote zai rika tace kimanin Ganga 650,000 a kowace rana (BPD) , Dangote Sugar Refinery, Numan and Tunga Operations, Dangote cement Plc. da NASCON Allied Plc, za su iya shiga cikin tsarin Nahiyar don ƙarin tasiri a tattalin arziki.

 

Babban Daraktan kungiyar masu masana’antu ta kasa Engr. Mansur Ahmed ya shaida wa manema labarai cewa Kano babbar cibiya ce ta kasuwanci a nahiyar Afirka, kuma bikin baje kolin na sake baiwa kamfanin damar yin amfani da damarsu wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje .

 

Da yake zantawa da manema labarai tun da farko, Darakta Janar na KACCIMA Mustapha M. Aliyu ya yabawa rukuni kamfanin Dangote bisa hadin kai da daukar nauyin bikin baje kolin a duk shekara.

 

Ya bayyana alakar dake tsakanin su da kamfanin Dangote da cewa kyakyawa ce Kuma daddiya ta Samar da cigaba.

 

Babban daraktan ya kara da cewa “Mun yaba da kokarinsa da kuma goyon bayansa waje ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Afirka.”

 

A wata sanarwa da kamfanin Dangote ta fitar ta ce kamfanonin da ke shiga karkashin rukunin kamfanin Dangote su haɗar da Dangote Cement, Dangote Sugar, NASCON, da Takin Dangote .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...