Daga Auwalu Shugaba U/uku
Dan majalisar dokokin jihar kano mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Hon. Lawan Rabi’u Journalist, ya bada tabbacin tallafawa makarantar gidan gona special primary school unguwa uku, don inganta harkokin koyo da koyarwa a makarantar.
” Insha Allah zan yi iya bakin gwargwadon ikona, inga matsalolin da suke damun wannan makaranta na kawar da su kona share muku hawaye insha Allahu rabbi”. Inji Lawan Rabi’u

Lawan journalist ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar tsofaffin daliban makarantar wadda yanzu aka fi sani da unguwa uku special primary school.
” A zahirin gaskiya naji dadin wannan ziyara kuma ta tunamin abubuwa da dama da na ga wadannan fuskokin, kuma na dada sanya kishin wannan makarantar a cikin zuciya ta” . Inji Dan majalisar
Da yake bayyana makasudin ziyarar tasu Shugaban kungiyar Malam Adamu Jafar yace sun ziyarci dan majalisar ne domin su yi masa fatan alkhairi kasancewar sa Dan kungiyar Kuma tsohon dalibin makarantar, Sanna su sada zumuncin da aka kafa kungiyar domin sa.
Yace sun sanar da shi tarin matsalolin da suka da baibaye makarantar domin ya taimaka ya magance wasu daga cikin matsalolin ko a kara inganta harkokin koyo da koyarwa a makarantar, kasancewar makarantar tana da dalibai masu tarin yawa.
Malam Habibu Abdullahi shi ne shugaban makaranta ta unguwa uku special primary school yace makarantar tana fama da matsalolin da suka hadar da karancin kujerun zama na dalibai kayan koyo da koyarwa da dai sauransu .