Atiku zamu marawa baya a zaben 2023 – Shugabannin kiristocin Arewa

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Gamayyar shugabannin Kiristoci da jagororin siyasa Musulmai da ga jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya, FCT, sun amince da mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya a zaben 2023.

 

Bayan taron shugabanni da wakilai da ga sassan arewacin kasar da su ka hada da shugabannin addinai da kungiyoyin mata da matasa, sun dauki matakin ne a Abuja jiya Juma’a a dakin taro na Atiku Abubakar da ke cibiyar Shehu Musa Yaradua.

Talla

Taron ya amince da rahoton kwamitin kwararru na IRS, karkashin jagorancin tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Mohammed Kumalia da Nunge Mele, SAN.

 

Idan dai ba a manta ba a ranar 8 ga watan Oktoba ne kungiyar shugabannin addinin kirista da musulmin Arewa ta kafa kwamitin da zai ba da shawarar tsarin da Najeriya ta dauka a zaben shugaban kasa na 2023.

 

Kudurin na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto kuma ministan albarkatun ruwa a zamanin gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo, Mukhari Shagari da D.D.Sheni su ka sanya wa hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...