Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar gudanarwar kafanin Amasis Broadcasting Services Ltd, masu gidan Talabijin na Tambarin Hausa sun nada Ibrahim Sani Shawai a matsayin sabon Manajan Darakta.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hukumar kuma wanda ya kafa gidan Tv Alhaji Ibrahim Makama.
Shawai wanda ya yi aiki a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata a matsayin Shugaban sashin yada labarai da hulda da jama’a na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na (KEDCO) Kuma zai fara aiki a sabon ofishin sa ranar 1 ga Janairu, 2023.

A sabuwar ofishin nasa, ana sa ran Shawai zai jagoranci harkokin yau da kullum na kamfanin, tare da yin aiki kafada da kafada da shugabannin sassan da kuma inganta alaka tsakanin ma’aikatan gidan Talabijin na Tambarin Hausa.
Har ila yau, zai tsara dabaru tare da aiwatar da manufofi a kamfanin na Amasis Broadcasting Services Ltd don inganta aiyuka da harkokin kasuwanci na kamfanin .
Tambarin Hausa TV “Amon Gaskiya” ita ce tashar talabijin a duniya ta farko da ke watsa shirye-shiryenta cikin harshen Hausa a Najeriya.
Tashar tana gudanar da labarai a kowacce sa’aa tare da gabatar da shirye-shirye iri-iri don jin daɗin masu sauraronta tashar.
Shawai, haifaffen Kano ne, wanda ƙwararren ɗan jarida ne kuma masanin dabarun sadarwa, ya yi aiki da kafofin yada labarai na gida dana kasashen waje wanda haka yasa ya kara gogewa a fannin.