Inganta Ilimi: Al’ummar Bebeji sun yabawa Hakiminsu saboda gina musu Makaranta

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

 

Al’ummar garin sabon bakin kunza ta Nasarawan kofa dake karamar hukumar Bebeji sun yabawa Hakimin bebeji Majidadin Rano Alh Tijjani Abdullahi, bisa kokarin da ya yiwa al’ummar unguwar Nasarawan kofa na Samar musu da ginin makaranta, saboda doguwar tafiyar da ‘yayensu suke yi a lokutan baya domin Neman ilimi.

 

Shugaban al’ummar yankin malam Ibrahim wada bebeji, Wanda yayi jawabi a madadin al’ummar garin ne ya bayyana haka a wata zantawa da manema labarai.

 

 “Muna mika godiyarmu ga hakimin da sakataren ilimin karamar hukumar ta bebeji saboda gudunmawar da suka bayar wajen samun Wannan makarantar wadda Ina yi Imani zata taimaka matuka wajen inganta Rayuwar matasan mu baki daya “. Inji Wada

Talla

 

Ibrahim wada bebeji, yace a lokutan baya, yaran Nasarawar kofa suna yin tafiyar kilomita uku domin zuwa neman ilimi, amma sakamakon gina wannan makaranta yanzu ba sai sun tafi wani guri ba, inda yace,wannan ba karamar nasara bace, ga al’ummar yankin da karamar hukumar bebeji baki daya.

 

Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a yankin da masu hannu da shuni da su tallafawa unguwar nasarawan kofa, musamman yan siyasa da su samarwa yankin makarantun da ‘yayensu za su rika zuwa domin neman ilimi addini da na Zamani don kara inganta Rayuwar al’ummar yankin.

Shin Yan adaidaita sahu sun bi sabuwar dokar hana su hawa manyan titunan Kano kuwa ? 

 

Ya kara da cewa rashin zuwan yara makaranta a halin yanzu ba karamar Matsala bace, Inda yace hakan aka jawo a samun batagari a cikin al’umma, wanda kuma hakan barazana ce ga tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummar yankin.

 

2023: Takarar Sha’aban Sharada nake goyon baya a ADP Kuma zan bashi gudunmawa har ya ci zabe – Rarara

Ibrahim wada bebeji, yayi kira ga Gwamnati, musamman ta karamar hukumar su, da ta taimakawa wannan yankunan da Karin makarantu kasancewar suna da karanci makarantun da ‘ya’yansu za su rika zuwa neman ilimi domin kaucewa shiga wasu matsalolin da ka iya tasowa a yankunan na karamar hukumar ta bebeji.

 

Yace,yanzu ne ya kamata a baiwa wannan yankunan tallafi da agajin da suka kamata,domin su ma su kurbi romon damaradiyya,ta hanyar nemawa ‘yayensu mafita domin ilimi shine gishirin rayuwa da ci gaban alumma a kodayaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...