Shin Yan adaidaita sahu sun bi sabuwar dokar hana su hawa manyan titunan Kano kuwa ? 

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi
Matuka baburan adaidaita sahu a jihar kano su bi dokar da gwamnatin jihar kano ta dora musu ta hana su bin wasu manyan titunan jihar.
Kadaura24 ta rawaito tun daren litinin din data gabata ne gwamnatin jihar kano ta karkashin hukumar Karota ta bada sanarwar dakatar da yan adaidaita sahun daga bin wasu manyan tituna a Kano.
Talla
Binciken da jaridar kadaura24 ta gudanar ya nuna cewa yan adaidaita sahun sun bi waccen doka, domin kuwa sun ƙauracewa titunan da aka ce ba’a son ganin su akai, wadanda suka hadar da tituna Ahmad Bello way by Mundubawa da Kuma tal’udu zuwa gwarzo.
Wakilin mu ya shaida yadda aka jibge jami’an hukumar karota domin ganin sun tabbatar da ba Wani dan adaidaita sahu da ya karya dokar.
Gwamnatin kano dai tuni ta samar da manyan motocin safa-safa domin maye gurbin yan adaidaita sahun da su a kokarin ta na Kara inganta harkokin sufuri a kano, haka Kuma gwamnatin ta yi alkawarin karo wasu motocin domin sanyasu a sauran manyan titunan jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...