Daga B Nasidi
Al’ummar garin Nata’ala dake cikin karamar Hukumar Tudun Wada sun zargi wani mai suna Malam Isyaku da Abdullahi Dan Chabe da karbe musu Gonaki da sunan Hakimin Tudun Wada ne ya aiko su.
A cewar mutanan Malam Isyaku da Danchabe kanzo musu da cewa wadannan gonakin ba nasu ba ne, a dan haka sai dai su sake saya ko a sayarwa da wani mai bukata.
Wasu daga cikin mutanan da lamarin ya shafa sun bayyana cewa Malam Isyaku da Abdullahi dan chabe sun karbi Kudi wasu dubu 300 wasu 500 inda wasu kuma 250.
Mutanan wanda adadin su ya kai kusan kimanin 15 sun ce, basu da wata sana’a data wuce noma, wanda itama gashi ana nema a ra basu da ita.
Abdullahi Danchabe guda ne daga cikin mutanan da ake zargi da karbe gonakin mutane tare da karbar kudade da sunan hakimin a zantawar mu dasu yayi karin haske game lamarin.

” Dakansu suke zuwa wajen malam Isyaka cewa suna so a mallaka musu takardun gurin don gudun abun da Zamani zai zo da shi, Kuma malam Isyaka yake yin jagoranci ake zuwa gaban Hakimi ake yin gaisuwa don siysarwa ake ba, mutum ne zai fadi iyakacin gonarsa hakimi ya mallaka masa takarda, amma ba sayarwa yake ba ba Kuma kwacewa yake ba”. Inji Abdullahi Danchabe
” Duk sirrin gonakan nan ba mai iya ba ka shi duk ƙasar Tudun Wada sama da malam Isyaka domin shi mazaunin Nata’Alah ne kuma ya rike akokin da ake aikin noman rani ma tun daga farkon anguza har ƙarshen PRP ta shekara akalla kusa 7 ko 10 a hannunsa”. Inji Danchabe
Duk kokarin da mukai naji daga bakin Malam Isyaku wanda Shi ne mutum na farko da mutanan suka ambata bai yadda mun yi magana dashi kusan karo biyu.
A hakan ne kuma ya sanya muka tuntubi sakataren Hakimin na Tudun Wada Malam Lamido Muhammad Domin ji daga bangaren hakimin inda Sakataren ke ya bayyana cewa wannan magana, ba haka take ba, domin hakimi bai san wannan magana ta sayar da gonaki ba, a dan haka dai ka mata yayi mu koma gurin wancan mutum mai suna Malam Isyaka domin a nan ne zamu sami cikakkun bayanai akan lamarin.
Al’ummar da abin ya shafa sun bukaci hukumomi dasu sanya baki domin karbar musu hakkinsu, don gudun abun da ka je ya zo.