Laifin Iyaye da shugabanni ne yasa matasa suke shiga bangar siyasa – Aminu Danjimmai

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

kungiyar ci gaban garin kwasamgwami dake karamar hukumar Gezawa ta bukaci matasan yankin da su kaucewa shiga bangar siyasa,musamman a wannan lokacin da ake ƙara tunkarar babban zaben shekarar 2023,.

 

Shugaban kungiyar matasan yankin Alh Aminu Danjimmai ne ya bukaci hakan lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 dangane da yadda harkokin zabuka suke karatowa na shekarar dubu biyu da ashirin da uku.

Talla

 

Alh Aminu yace kasancewar lokacin zabuka yana Kara karatowa, akwai bukatar kungiyar ta ja hankalin matasan yankin da ka da su bari wasu ‘yan siyasa su yi amfani da su don cimma muradunsu na siyasa da kuma sanyasu a cikin yanayi na damuwa da zai haifar musu da matsaloli a rayuwarsu.

Ana amfani da sunan Hakimin T/Wada ana kwace mana gonakin mu – al’ummar wani gari suka koka

 

” Duk lokacin da yan siyasa suka samu damar darewa kan mulki ba za su tuna da matasan ba, su da ‘ya’yansu ne kadai suke amfana da damar, sai kuma yanuwan matansu da sauran wadanda suke bukatar su zo kusa da su, akan me dan talaka zai bari ayi amfani da shi kuma a cutar dashi don Jin dadin wasu”. Inji Aminu 

 

Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan Nijeriya

Yace ba’a hana matasan yi zabe ba, amma ya kamata su yi karatun ta nutsu wajen sanin wanne ma shugaba ya kamata su zaba, domin inganta rayuwarsu a nan gaba.

 

“An Dade ana ruwa kasa na shanyewa akan al’amuran da suka shafi harkokin matasa da kungiyoyin matasa, kasancewar matasa sune kashin bayan kowacce alumma, don haka dolene a ci gaba da kiraye kiraye akansu don su gujewa shiga bangar Siyasa da shaye-shayen kwayoyi”.

 

Haka zalika,ya yi kira ga iyaye da su iya kokarinsu domin sauke nauyin daya rataya a wuyansu, kasancewar Allah subahanahu wata’ala sai ya tambayesu ranar gobe alkiyama, ya kuma kara da cewa iyaye suna da rawar takawa wajen fadakar da ‘ya’yansu ta hanyoyi da dama su kuma fahincesu tare da kaucewa shiga bangar siyasa.

 

Ya kuma shawarci mahukunta da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin siyasa, da su fito da wasu hanyoyi da za su saka matasa akan gwadabe nagari da zai janye hankalin matasa daga bangar siyasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...