An sace kayan fitar angwanci na wani ango a Kano

Date:

 

Ɓarayi sun fasa shagon wani tela, mai suna Ali Isma’il a unguwar Kundila a jihar Kano, inda su ka yi awon-gaba da shaddoji, yadika da sauran kayayyaki.

 

Daily Nigerian ta jiyo cewa da ga cikin kayayyakin da ɓarayin su ka sace har da set shida na wani ango, mai suna Junaidu Muhammad duk a nan unguwar ta Kundila.

 

Wannan lamari ne kwanaki uku kafin ɗaurin auren Junaidu, inda ya shaida wa manema labarai cewa ya kai ɗinkin kayan ne domin fitar angwanci.

Talla

 

Da ya ke wa da manema labarai, shima telan, ya ce ya tashi da safe ne dai ya tarar an ɓalle shagon na sa an kuma yashe kayayyaki sama da set talatin na kwastomominsa.

 

“Kaya ne a aka dauka dinkakku da waɗanda ba dinkakku ba. Sun haɗa da shaddoji da yadika. Dinkakku da aka sace sun kai set 16. Wadanda ba dinkakku ba kuma sun kai sama da set 30,” in ji Isma’il.

 

Daga ciki, a cewar telan, har da na shi wannan ango da ke shirin kece raini kafin da kuma bayan bikin nasa.

 

Sai dai kuma telan ya ce ya ji daɗi sabo da duk kwastomomin da abin ya shafa, har da shi angon, sun ɗauki na damo.

 

Yanzu haka dai jami’an tsaro na yankin unguwar sun ce sun fara gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...