Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Mohammad Badaru Abubakar MON, mni ya mika tutoci jam’iyyar APC ga ‘yan takarar Santoriyar Jigawa ta arewa maso yamma wato shiyyar Gumel.
Dubban magoya bayan jam’iyyar da manyan ‘ya’yan jam’iyyar na daga cikin wadanda suka halarci taron wanda ya gudana a karamar hukumar Gumel ta jihar.
Da yake jawabi ga magoya bayansa, Gwamna Badaru Abubakar ya bukaci al’ummar jihar Jigawa da su zabi jam’iyyar APC daga sama har kasa, domin a cewarsa jam’iyyar ta samar da dimokuradiyya ga al’ummar jihar.

Cikin sanarwar da kwamishinan aiyuka na musamman na jihar Jigawa Hon. Auwalu Danladi Sankara ya fitar ta sahihin shafinsa na Facebook, yace gwamnan ya kara da cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da ba da fifiko a bangaren ilimi, lafiya, samar da ababen more rayuwa, da karfafa tattalin arziki.
Dan takarar gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar ya tabbatarwa al’ummar jihar Jigawa cewa zai dora kan aiyukan cigaba ga gwamnan Badaru ya faru domin cigaban jihar idan har al’ummar jihar suka zabe shi matsayin Gwamnan Jigawa.
A cewar dan modi, gadon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar bai dace ga rago ba wadanda basu San daga Inda aka taho ba da Inda za’a kai jihar Jigawa, ta bangarorin lafiya, aikin noma, Samar da aiyukan yi ga matasa maza da mata da Samar da ababen more Rayuwa.