Buhari zai buɗe aikin tono man fetur a Bauchi da Gombe

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin tono man fetur a jihohin Bauchi da Gombe.

 

An dai gano tarin arzikin man fetur a jihohin biyu shekaru biyu da suka gabata

 

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato ƙaramin ministan man fetur na ƙasar Timipre Sylva, na cewa ”Za a gudanar da bikin fara tono man ranar Talata 22 ga watan Nuwamba Inda shugaba Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta”

 

Talla

A shekarar 2016 ne kamfanin mai na ƙasar NNPC ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasar, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Niger

 

A yayin da ƙasar ke dogara da man da ake tonowa daga yankin Niger Delta, Wannan shi ne karo na farko da za a fara tono man a yankin arewacin ƙasar, bayan da rikicin Boko Haram ya hana yunƙurin tono man a jihar Borno

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...