Daga Maryam Abubakar Tukur
Shirin bunkasa noma da kiwo na Jihar Kano, KSADP, ya fara ayyukan gine-gine da suka kai N2, 509, 343, 144. 10 a wurin kiwo na Dansoshiya da ke karamar hukumar Kiru.
Shugaban shirin KSADP, Malam Ibrahim Garba ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a Dansoshiya tare da mika wuraren aikin ga ‘yan kwangila.
Wuraren da za’a gina, da nufin mayar da wurin zuwa wurin kiwo na zamani, sun hada da samar da kadada 2,000 na kiwo, da filin kiwo mai fadin hekta 1,000, za’a gina madatsar ruwa, sai gina katanga mai tsawon kilomita 25, da kuma gina titina mai nisan kilomita 20 da samar da na’urorin kashe gobara.

Sauran sun hada da gina masallaci da gina rukunin ajujuwa uku, kantin sayar da kayayyaki, gina karamar kasuwa, asibitin dabbobi da kayan aiki, da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda biyar.
“Muna gudanar da wadannan ayyuka, wadanda za su canza rayuwar makiyaya, domin cika burin gwamnatin jihar kano na samar da tsarin Ruga”, in ji Kodinetan aikin.
Shirin na Ruga na yunkurin tsugunar da iyalan makiyaya da ke yawo tare da samar da ababen more rayuwa da za su ba su damar jin dadin Inda suke.
Cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran shirin Ameen K Yassar ya aikowa kadaura24, yace Malam Ibrahim Garba ya bayyana cewa baya ga kwangilolin da aka ambata, aikin zai gina tare da samar da a kalla cibiyoyin tattara madara na zamani guda biyar a fadin Dansoshiya a wani bangare na kokarin kara darajar dabbobin su.
Ya kuma bukaci makiyayan da su ba ‘yan kwangilar hadin gwiwa don ganin an kammala ayyukan cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa dole ne ‘yan kwangilar su bi dukanin ka’idojin kwangila na samar da ingantaccen aiki .
Da yake jawabi a madadin makiyayan, shugabansu, Ardo Abubakar Rabo da sakataren kungiyar ci gaban al’umma ta FULDAN, Muhammadu Majo, sun yi alkawarin bayar da hadin kai sosai don ganin an kammala ayyukan kamar yadda aka tsara.