Gwamnatin Kano tana raba gidajen sauro sama da miliyan 8 don kawar da maleria

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

 

Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar kula da cutar zazzabin cizon sauro ta Global Fund, ta kaddamar da rabon gidajen sauro a jihar nan wanda yawan sa yakai sama da miliyan takwas da ake rabawa masu karamin karfi a jihar.

 

Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace aikin na shekarar 2022 an kaddamar da shi ne da zummar yakar sauro ta hanyar raba gidan sauro mai dauke da magani a lungu da sako na kananan Hukumomin 44 dake jihar kano.

 

Gwamnan wanda mataimakinsa kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya bayyana haka ne a ranar Laraba a garin Gaya, yayin kaddamar da shirin raba gidajen sauro mai dauke da magani da kuma allurar riga-kafin zazzabin shawara a jihar Kano.

 

A cewarsa, akalla ma’aikatan wucin gadi sama da dubu 20 aka dauka domin gudanar da aikin kuma yanzu haka an raba gidajen sauro sama da dubu uku da dari shida a cikin unguwanni dari hudu da tamanin da hudu a fadin jihar.

Talla

Ya kuma bayyana cewa rabon gidajen sauron abin a yabawa kokarin da gwamnatin jihar Kano ke yi ne na inganta lafiya da walwalar al’ummar jihar, inda ya ce gwamnatin jihar tana amince da siyowa da rarraba kayan yaki da cutar zazzabin cizon sauro kyauta a kowane wata.

 

“Don haka ina kira ga al’ummar da ke dake tsakanin wadannan shekarun da su yi amfani da wannan damar ta hanyar cin gajiyar aikin rigakafi domin yin alluran rigakafi zai taimaka wajen magance cutar zazzabin cizon sauro.” inji Gawuna

 

Sanarwar da babban Sakataren yada labaran mataimakin gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24, yace wadanda suka halarci taron sun hada da Mai Martaba Sarkin Gaya Alh.Aliyu Ibrahim, Shugaban Ma’aikatan Kano Alh.Usman Bala Muhammad, Kwamishinan Lafiya Dr.Aminu Ibrahim Tsanyawa, Wakilan Abokan Cigaba da sauran masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...