Gwaji kafin aure ita ce babbar hanyar rage yawan masu cutar Sikila – Maharazu Gizina

Date:

Daga Ibrahim sani Tana

 

Kungiyar dake wayar da kan al’umma dangane da yin gwaji kafin aure ta jihar Kano, ta sha alwashin ci gaba da wayar da kan matasa maza da mata mahimmancin yin gwaji kafin aure domin samun ‘ya’yan masu cike da koshin lafiya a jihar Kano da ma kasa baki daya.

 

Shugaban kungiyar na jihar Kano, Alhaji Muharazu Adamu ibrahim gizina ne, ya ba da tabbacin hakan a lokacin da kungiyar ta ziyarci makarantun sakandiren yan mata ta yakasai dake birnin kano da Kuma ta Dorayi dake karamar hukumar Gwale.

 

Yace sun kai ziyara makarantun ne domin ci gaba da wayar da kan matasa amfanin yin gwaji kafin aure, domin kaucewa haifar yara masu dauke da cutar amosanin jini da sauran cututtuka.

Talla

 

Muharazu Adamu yace kungiyar an kafata ne, karkashin jagorancin matasa masu kishin al’ummar jihar kano da Najeriya, kasancewar iyaye suna mutukar shan wahala idon suka samu ‘ya’ya masu dauke da cutar amosanin jini, ta fannin aljihunsu da jikinsu, wanda ba karamar dawainiya bace a garesu ba.

 

Shugaban kungiyar ya bukaci Gwamnatin tarayya da ta jiha da sauran shugabanni masu rike da sarautun gargajiya da su taimakawa yunkurin kungiyar na ci gaba da wayar da kan matasa maza da mata amfanin yin gwaji kafin aure domin kaucewa samun yara marasa koshin lafiya.

 

Yace akwai bukatar ci gaba da wayar da kan al’umma duba masu dauke da cutar amosanin jini suna mutukar shan wahala a wannan lokaci na hunturu dake tafe, dole al’umma suna bukatar fadakarwa.

 

A jawabinsa mataimakin shugabar makarantar yan mata dake unguwar yakasai, malam sadik Tijjani, ya nuna mutukar farin cikinsa bisa wannan ziyarar wayar da kan matasa amfanin yin gwaji kafin aure, domin Mata sune wadanda ya kamata a wayarwa da kai domin kaucewa fadawa cikin irin wannan yanayi.

 

Itama anata jawabin, shugabar makarantar yan mata ta Dorayi dake karamar hukumar Gwale, Hajiya Halima Imam, ta jaddada aniyarta na baiwa shugabancin kungiyar goyan bayan daya dace, domin samun damar cin nasarorin da aka sanya a gaba a gaba, na wayar da kan matasa maza da mata amfanin yin gwaji kafin aure.

 

Daga karshe ta shawarci iyaye da su kasance masu kulawa da lafiyar wadanda suka zuwa domin neman auren yayansu duba da wahalar dake tattare da cutar amosanin jini da sauran cututtuka da ake kamuwa da su ta hanyar auratayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...