Wata Kungiyar kare hakkin dan Adam ta bukaci a maida da wani alkali bakin aiki ko su dauki mataki

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights and Social Justice ta bukaci alkalin alkalan jihar Kebbi Mai girma Muhammad Sulaiman Ambursa da ya gaggauta Maida Wani alkali mai suna Mustapha Umar Maccido baki aikin sa ko su dauki matakin Shari’a.
Hakan na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 08/11/2022 wadda Shugaban kungiyar ta kasa Saeed Bin Usman ya sanyawa hannu kuma aka aikawa alkalin alkalan jihar Kebbi.
Wasika ta yi zargin cewa cikin wata October da ya gabata magatakardar babban kotun jihar Kebbi Hussaini Abdullahi Zuru, a taron manema labarai da ya kirawo yace sun dakatar da mai Shari’a Mustapha Umar Maccido Saboda laifin kin zuwa aiki da kuma shiga harkokin kashin kansa a jihohin Kaduna Lagos Zaria da Abuja, ba kuma tare da bayyana wata kwakwkwarar hujjaba akan zargin da suke yi masa.
Talla
Wasikar ta kara da cewa an yada labaran a kafafen yada labarai da na sada zumunta wanda hakan cin zarafi ne ga mai Shari’a Mustapha Umar Maccido, wanda ya jawo masa tsangwama a cikin al’umma kuma “muna zargin an yi hakane da gayya don a tozarta shi bisa abun da ba’a da hujja akan sa”.
” Sakamakon abun da akai yiwa mai shari’ar Maccido, Muna kira ga wadanda abun ya shafa da su gaggauta ba shi hakuri a jaridu da kafafen yada labarai na kafafen yada zumunta cikin kwanaki biyu ko Kuma kungiyar ta ɗauki matakin Shari’a akan lamarin”. Inji Wasikar
Tun da fari dai wasikar ta bayyana cewa mai shari’a Mustapha Umar Muccido me ya sanar da su halin da ake ciki, kuma su amatsayin su na masu kare hakkin dan Adam zasu iya bakin kokarin su wajen kwato hakkin mai shari’ar Maccido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...