Daga Rahama Umar Kwaru
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma da su rinka sanya ‘ya’yan su a makarantu Islamiya domin rabauta da albarkarsa duniya da lahira.
Sarkin ya bukaci hakan ne a wajan taron bude Karatun Musabakar karatun alkur’ani mai tsarki da aka gudanar a makarantar koyar da harshan larabci ta S A S dake Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake bukatar al’umar jihar Kano da sauran Musulmi a ko ina suke a duniya, da su yawaita karatun Alkur’ani a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Mai Martaba Sarkin na kano ya kuma yi kira ga mutane da su dukufa wajan yin addu’o’in samun zaman lafiya a lokutan zabe mai zuwa Saboda ayi lafiya a gama lafiya tare da neman Allah ya zaba mana shugabanni nagari.
cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Sarkin ya kuma nuna damuwar sa a kan rashin shigar wasu kananan Hukumomi cikin tsarin shirin musabukar na bana.
Yace lallai wannan abune marar dadi, inda yayi fatan za’a bincika domin a fahimci dalilan da ya kawo hakan domin gyarawa a nan gaba.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yabawa gwamnatin jihar kano bisa daukar nauyin musabakar da take duk Shekara, tare da bayar da dukkan gudumawar data kamata tun daga matakin kananan hukumomi zuwa ta duniya baki daya.
A nasa jawabi shugaban hukumar Shirya musabakar al’qur’ani ta jihar Kano wanda shugaban kwamatin tsare-tsaren musabukar Malam Abdurrahaman Tijjani ya wakilta, yace a bana kananan hukumomi hudu ne basu shiga cikin shirin musabakar ba, wadanda suka hadar da karamar hukumar Birni, Rogo Garin Malam da kiru da kuma Doguwa.