Kotu ta bada umarnin aikewa da shugaban EFCC zuwa gidan yari

Date:

 

Mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aike shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC zuwa gidan yari bisa laifin ƙin bin umarnin kotu.

 

Alkalin ya kuma umurci Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar da ya tabbatar da an aiwatar da hukuncin.

Talla

Oji ya ba da umarnin ne a ranar 28 ga Oktoba, in da a ka raba wa manema labarai a Abuja kwafin umarnin.

 

AVM Rufus Adeniyi Ojuawo ya gabatar da korafi a kan gwamnatin tarayya mai lamba FCT/HC/M/52/2021 a kara mai lamba FCT/HC/CR/184/2016.

 

AVM Ojuawo ta bakin lauyansa R.N. Ojabo, ya nemi umarnin daure Shugaban Hukumar EFCC a gidan yari.

 

Hakan ya bayu ne bisa rashin biyayyarsa ga kotu, ya kuma ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018.

 

Daily Nigeria ta rawaito Kotun ce ta umarci EFCC, Abuja da ta mayar wa wanda ya shigar da korafi motsa kirar Range Rover (Supercharge) SUV da kudin ta ya kai Naira miliyan N40.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...