Bata sunan Ganduje: Kotu ta yankewa yan TikTok hukuncin bulala 20 da shara

Date:

Daga Umar Ibrahim Sani mainagge

 

Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala ashirirn-ashirin tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu ashirin kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.

 

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kokarin tada fitina a cikin al’umma, sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin na tiktok din su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kan bata masa suna.

 

Matasan Mubarak Isa Muhammad da aka fi sani da Mubarak Pikin, da Nazifi Muhammad Bala, na shirya gajeren bidiyon barkwanci, inda akasari suke kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane.

Talla

Mabarak Unique Pidkin da abokinsa za kuma su share harabar kotun Norman Saland baki dayanta har na tsawon wata guda.

 

Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, na gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina,

 

Inda kuma suka amsa laifinsu al’amarin da yasa aka yanke musu hukuncin, Lauya mai gabatar da kara ya ce an kama matasan tun makon jiya inda aka gurfanar da su a gaban kotun, kafin daga bisani kuma aka aika su gidan yari.

 

Matasan dai suna hannun jami’an tsaro har sai sun cika wadannan ka’ido kafin a sake.

 

Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci shi ne lauyan matasan ya kuma gode wa kotun majistaren bisa sassaucin da ta yi musu game da hukuncin, don haka ma basu kalubalanci hukuncin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...