Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Martaba Sarkin Jama’are dake jihar Bauchi Alhaji Nuhu Ahmad Wabi ya jaddada alakar dake akawai tsakanin Masarautar Jam’are da ta Kano tare da cewa alakace mai dunbun tarihi.
Sabon Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR a fadarsa a safiyar yau Lahadi.
Yace tun zamanin Sarkin Kano na shida a daular Sarakunan fulani Masarautar Jama’are da ta Kano suke da alaka mai karfi a tsakaninsu.

Ya kuma yabawa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa ziyarar da yakaiwa Marigayi tsohon Sarkin Jama’are dake Jihar Bauchi.
Daya ke jawabi, Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, ya ja hankalin Sabon Sarkin na Jama’are da yaji tsoran Allah yayin da yake gudanar da mulkin sa a masarauta wajen kula da hakkin al’ummar sa.
A Cikin sanarwar da sakataren yada labarai na Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 yace Sarkin ya kuma bukaci sabon sarkin da sanya hakuri a cikin tsarin mulkinsa da kuma janyo “yan uwansa a jiki domin taimaka masa wajan gudanar da mulkinsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kuma hori yan’majalisar sabon sarkin su tabbatar sun nuna masa hanya madaidaiciya a cikin shugabancin nasa.