Malam Shekarau yace sun dinke barakar PDP a Kano

Date:

Yayin da ake ƙara kusantar lokacin babban zaɓe a Najeriya, jam’iyyun siyasa na ƙasar na ci gaba da aiki domin ɗinke ɓarakar da suke da ita gabanin zaɓen.

A jihar Kano, jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da sabon shugabancin riƙon ƙwarya domin magance mastsalolin da jam’iyyar ke fama da su a jihar a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben 2023.
Jam’iyyar a mataki na kasa ta nada tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau a matsayin wanda zai jagoranci sulhu tsakanin ‘ya’yanta a jihar.
Kuma cikin hirarsa da BBC Shekarau ya ce yanzu sun ɗinke duk wata baraka da ke damun jam’iyyarsu a baya.
“Ko wa ya jingine sabanin cikin gida ya yarda da cewa uwa daya uba daya muke, musammam abin da ya danganci sabanin da aka ratso a baya.
Talla
“Sai ko wanne dan jam’iyya ya ji a ransa wajibi ne ya yi aiki da hukuncin kotu da na uwar jam’iyya domin cimma nasara.
“An kafa mana shugaban cin riko domin su rike shugabanci zuwa bayan zabe, wanda bayan nan za a yi zabe somin samun jagororin da za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyar zuwa shekaru hudu,” in ji Shekarau.
Ya ce nasarar da suka samu shi ne duka bangarorin da ba sa ga maciji da juna na jam’iyyar sun halarci zaman da suka yi na sulhu da kuma kaddamar da shugabancin riƙon ƙwaryar.
Shekarau ya ce gabanin wannan taron ya zauna da duka ‘yan takarar gwamnan da suke wannan rikici bangaren Muhammad Abacha da na Sadik Wali ya musu nasiha cikin mutane, ya kuma tunasar da su cewa dukkansu abu daya suke yi wa.
Ya yi imanin cewa idan PDP ba ta yi nasara ba faduwar su ce baki daya, babu wanda zai ce ya yi nasara, a cewarsa tun tuni an gama da wannan baraka. Wakilin BBC ya tambayi Shekarau game da rikicin shugabancin jam’iyyar na kasa da aka ce batun na gaban ko tun koli.
Shekarau ya ce “uwar jam’iyya ta kasa ba ta sanar da mu hukuncin kotun koli ba idan aka yi hukunci tunda akwai lauyoyin jam’iyya su ne za su karbo umarnin kotun a zauna a fassara umarnin kotun sai a sanar damu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...