Daga Auwal Alhassan Kademi
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya sake jaddada kiran cire Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Wike ya bayyana cewa ya amince da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP da kuma Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Ribas a matsayin dan takarar mataimakin Atiku, amma yace dole sai Ayu yayi murabus.
Ya yi nuni da cewa murabus din Ayu shi ne kadai hanyar sulhu a jam’iyyar.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin ’yan takarar Gwamna, da Sanata, na Majalisar Wakilai, da na Majalisar Wakilai, da shugabannin Jam’iyyar na kananan hukumomi a gidansa da ke Rumueprikom.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na Wike, Kelvin Ebiri, ya fitar, ta ruwaito shi yana cewa: “Mun kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa, shin wike yace a cire dan takarar shugaban kasa? Ko nace a cire dan takarar mataimakin Shugaban Kasa? To, me kuke rokona? Abin da kawai nake cewa, kuma zan ci gaba da cewa, shi ne ba dai dai bane a ka dauki shugaban kasa, da shugaban jam’iyya duk a bangare guda.
Ba wanda zai ce nayi gaskiya. Idan na ce a cire dan takarar shugaban kasa, ko idan na ce a cire dan takarar mataimakin shugaban kasa.