Kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta kori ƙarar gwamnati tarayya a kan jagoran ƙungiyar ƴan aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ta hanyar yin watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Tawagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari’a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari’a tun farko.

Hukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka.

Alkalan sun ce an dawo da shi Najeriya ne ba bisa ƙa’ida ba.
