Da dumi-dumi: ASUU ta janye yajin aikin da ta yi watanni takwas tana yi

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi, makamar yadda jaridar The PUNCH ta rawaito.

Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, wakilin jaridar ya tattaro cewa an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa ta kungiyar da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.

Talla

Da yake zantawa da Majiyar Kadaura24, Wani da ya nemi a sakaye sunansa wanda kuma yana cikin taron, yace “Eh, an dakatar da yajin aikin”.

Talla

Da aka nemi karin bayani, majiyar ta ce, “Shugaban ASUU zai fitar da wata sanarwa a hukumance da safiyar nan”.

Talla

Kungiyar malaman ta fara yajin aikin ne a ranar Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022.

 

Karin bayani na nan tafe…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...