Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar kasuwar kofar Wambai ta jaddada kudirinta na ci gaba da bijiro da managartan tsare -tsare domin inganta kasuwancin al’ummar kasuwar da bunkasa tattalin arzikin kasuwar da jihar kano baki daya.
Babban sakataren kungiyar kasuwar Alh. Jamilu Yahaya Ibrahim ne ya bayyana haka a lokacin da yake karin haske ga manema labarai dangane da nasarorin da shugabancin kungiyar kasuwar ya samu tun daga farkon kama mulkinsa zuwa yanzu.
Yace kungiyar ta samar da zaman lafiya tsakanin al’ummar dake gudanar da kasuwanci da bakin da suke shiga daga wasu wuraren kasuwar domin yin ciniki da samar da tsaron dukiyoyin yan kasuwar da nemowa yan kasuwa hanyoyin bunkasa jarinsu.
Sakataren yace, kungiyar ta kuma shigewa ‘yan kasuwa gaba wajen samar musu da rumfuna a kasuwar Dalar Gyada domin ganin sun fadada kasuwancinsu da baiwa wanda bashi da rumfa damar mallakar tasa da shigo da tsarin tallafawa masu karamin karfi da marayu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Jamilu Yahaya ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su tallafawa kungiyoyin ‘yan kasuwa dake kasar nan duba da yadda kasuwanci yake neman durkushewa a Najeriya, wanda hakan zai haifar da rashin ayyukan yi a fadin kasar nan.
Haka zalika, ya bukaci al’ummar kasuwar da ci gaba da baiwa kungiyar kasuwar cikakken hadin kai da goyan bayan da ya dace domin ci gaba da bijiro da managartan shire – shiryen da zasu habaka kasuwancinsu a kodaushe, wanda yin Hakan zai Kara farfado da tattalin arzikin jihar kano.