Daga Auwal Alhassan Kademi
Dubban ƴan Kwankwasiyya ne su ka yi dafifi domin tarbar da kuma gane wa idonsu buɗe ofishin jam’iyyar adawa ta NNPP da ɗan takarar ta na shugabancin ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso zai yi a jihar Kano a yau Lahadi.
Kadaura24 rawaito cewa magoya baya sun dafifi su na tsimayen tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP domin buɗe ofishin a unguwar Sharada da ke birnin Kano.
Tuni dai gurin ya rincaɓe da magoya baya, babu masakar tsinke, inda hakan ya haifar da cunkoson ababen-hawa a yankin da ma titunan da su kai haɗaka da Sharada.
A yayin da yake jawabi a wajen taron Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso yace wannan taron ‘yar manuniya ce da abun da zai faru a babban zaben shekara ta 2023.
Ya bukaci matasa a ranakun zabe su fito su zabi jam’iyyar NNPP sannan su tsaya domin kare abun da suka zaba domin inganta Rayuwar matasa a jihar kano.