Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar kula da kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), reshen jihar Kano, ta ce ta kama sama da motoci dubu uku wadanda ba su da lambobi daga watan Agusta zuwa yanzu.
Kwamandan shiyya na hukumar, Zubairu Mato ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da Radio Nigeria a Kano.
A cewarsa, rajistar motoci na da matukar muhimmanci wajen inganta tsaro da daƙile laifuka da sauran munanan ɗabi’u na al’umma.
Mato ya ƙara da cewa, an samu raguwar hadurran kan tituna a jihar, domin a bana hukumar ta sami rahoton hadururruka 100 da doriya ne kadai, ba kamar bara ba da aka sami sama da 300.
Da zarar na zama gwamnan kano zan biya yan fansho hakkokin su – Dan takarar PRP
Zubairu Mato ya danganta raguwar, ga tsauraran dabaru da hukumar FRSC ta jihar Kano ta kaddamar.
“Muna da motocin da ke kawar da kanana da manyan motocin dakon kaya da suka lalace a hanya domin kare duk wani cikas da ka iya faruwa a kowane lokaci.”
Sai dai ya nanata cewa, hukumar ta gudanar da wayar da kan jama’a a garejin motoci, da wuraren tarukan Jama’a a fadin masarautun Jihar guda biyar da kuma gangamin wayar da kan masu ababen hawa.
Kwamandan shiyar ya ce FRSC ta kafa kotunan tafi da gidanka domin dakile gudun wuce sa’a Akan tituna da yin lodin da ya wuce kuma da amfani da waya yayin tuki da duk wasu batutuwan da suka shafi karya dokokin hanya.
Dangane da batun daukar matakin gaggawa kan hadurran tituna, Zubairu Mato ya bayyana cewa, hukumar na aiki ba dare ba rana domin bayar da agajin gaggawa ga wadanda hadari ya rutsa da su, da kuma kai su asibitin hukumar da ke Chiromawa, wanda ke ba da magani kyauta ga wadanda abin ya shafa.
Sai dai kwamandan ya gargadi direbobi da su daina aikata laifukan da suka shafi tuki, kamar tuki Cikin Maye, da shan miyagun kwayoyi, da gudun wuce kima, da kuma tuki ga wadanda suke Kasa da shekaru 18, da yin waya yayin tuk