Daga Maryam Abubakar Tukur
Jam’iyyar NNPP, reshen jihar Kano, tace ta bankado wani shirin da jam’iyyar APC mai mulki ta keyi, na rage yawan mutanen da ke da katin zabe na dindindin (PVC) a jihar, ta hanyar karbe katinan zaben daga wajen masu su.
Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta yi nuni da cewa a karon farko a tarihin mulki a jihar kano, gwamnati ci ta mayar da al’amuran gwamnati tamkar na iyali, kamar yadda ake gani a manufofin gwamnati da nade-naden mukamai, inda ta kara da cewa abin ya fi daukar hankali shi ne yadda dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya rantse da cewa zai dora da duk abun da ake yi a wannan gwamnatin.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a matsayin wani bangare na nuni da yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da babban nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa ta hanyar zama abin ban tsoro da son zuciya, son rai, cin zarafi da kuma wadatar da kai, kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, a karshen taron karawa juna sani na jam’iyyar NNPP da gwamnoni da sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da ‘yan takarar majalisar jiha da shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a ranar 15 ga Satumba, 2022 a DUTSE ROYAL HOTEL, MAIDUGURI ROAD, a Kano.
A cewar sanarwar bayan taro da aka fitar ga yan jaridu mai dauke da sa hannun shugaban taron, Honorabul Garba Diso, da sakataren kungiyar Dakta Hamisu Sadi Ali, cewa an shirya taron bitar ne don neman mafita cikin gaggawa game da barazanar rashin da’a, da yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a kan lamarin. cikin gaggawa a buga tare da liƙa sunayen duk PVCs ɗin da ba a karba ba.
Daga cikin batutuwan da taron bitar ya yi tsokaci akai sun hada da lalacewar Ilimin da ya biyo bayan Rufe makarantun hadin gwiwa da na kwana; rashin biyan duk kudin jarrabawar da gwamnatin jihar ta yi ga WAEC, NECO, da NBAIS; jinkiri da rashin biyan alawus na tallafin karatu ga daliban kasashen waje da na gida; da kuma samar da kyakyawan yanayi ln koyo da koyarwa a cikin harabar makarantun ta hanyar gina shagunan kwana a makarantu kamar Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.
Don haka taron ya nuna matukar damuwarsa dangane da ambaliyar ruwa da rugujewar gine-ginen da suka faru a baya-bayan nan a kasuwannin Kantin Kwari da Civic Centre wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi da dai sauransu, kamar yadda ya jajantawa duk wadanda abin ya shafa, a madadin jagoran Kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, shuwagabannin jahohi, jam’iyyar, yan takarar gwamna da mataimakin sa, Sanata, dan majalisar wakilai, da kuma yan takarar majalisar jiha.
A karshe taron ya bayyana goyon bayan jam’iyyar NNPP a jihar baki daya, inda ya jaddada cewa lallai zaben 2023 ya sha bamban da wanda ya gabata sannan kuma jam’iyyar za ta yi duk abin da za ta iya a bisa tsarin doka don ganin zaben 2023 ya gudana cikin ‘yanci. , gaskiya kuma wanda kowa zai amince da shi.