Ra’ayin Bala Ubandoma unguwar jeka da fari a Gombe
Alamu na cigaba da nuna cewa wankin hula zai kai jam’iyyar adawa ta PDP dare a jihar Gombe a dai-dai lokacin da a ke cigaba da tunkarar zabukan gama-gari na shekarar 2023.
Kafun wannan lokaci, yan watanni kalilan da suka gabata, masu sharhi akan al’amuran siyasa da ma mu yayan jam’iyar na ganin cewa jam’iyyar tamu ta PDP zata kai bantenta a zaben 2023 dake tafe, ganin yanda farin jinin Gwamna Inuwa Yahaya da jam’iyyarsa ta APC ke disashewa a jihar, a yayin da jam’iyyar PDP kuma ke matukar tashe, hakan ba zai rasa nasaba da irin aiyukan da gwamnonin jihar a karkashin PDPn su ka shinfida ba.
Amma a baya-bayannan, al’amura sun sauya a siyasar ta Gombe, inda reshe yake kokarin juyawa da mujiya.
A baya, anga yanda masu rike da mukamai a jam’iyyar APC da jami’an Gwamnatin jihar suke ajiye mukamansu, su kuma sauya sheka zuwa jam’iyyar mu ta PDP.
‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda ake zargi da kisan dan Kabiru Gaya
Amma tun bayan zabubbukan fidda gwani da su ka gudana kimanin watanni uku da suka gabata, reshe ya juya da mujiya, inda shugabannin jam’iyyar mu ta PDP a matakai daban-daban, da wasu masu ruwa da tsaki a harkokin jam’iyyar suke ajiye mukamansu na jam’iyyar su kuma tsallaka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
A yan makonni da suka gabata, anga inda shugabannin jam’iyyar ta PDP a karamar hukumar Kaltungo har guda 5 da suka hada da Sakataren Jam’iyyar na karamar hukumar, shugaban matasa na karamar hukumar, babban lauyan Jam’iyya na karamar hukumar da kuma sakataren tsare-tsare na karamar hukumar suka ajiye mukamansu kuma suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ban janye daga takarar majalisar tarayyar Gezawa da Gabasawa ba – ‘Yar takarar PDP
Irin haka ya sake kasancewa a karamar hukumar Dukku, inda nan ma jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar PDP na karamar hukumar tare wasu jigajigan jam’iyyar suka ajiye mukamansu kuma suma suka fice daga jam’iyyar ta PDP.
A farkon satin nan da muke ciki, daya cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta PDP a karamar hukumar Gombe, Umar Dono Muazu shima ya tsallaka zuwa jam’iyyar APC.
Wannan abubuwa da ke ta faruwa ko kadan ba zai yi wa duk wani mai kaunar jam’iyyar jigajigan jam’iyar a jiha da ma tarayya dadi ba.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2022/09/FB_IMG_1663151273474-191x300.jpg)
Kuma na sani, kamar yadda kowanne mai kishin PDP ya sani cewa muddin ba a tashi tsaye domin daukar matakin shawo kan barazana da wannan jam’iyyar ke fuskanta ba akwai yayanta da dama da ke shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Akwai bayanai da ke cewa Gwamnan jiha Inuwa Yahaya, da wasu jiga-jigan gwamnatin na amfani da irin baraka a PDPn wajen yin ganawan sirri da wadannan jigajigai na jam’iyyar ta PDP a nan Gombe da kuma birnin Abuja, inda suka fahimci juna kuma suka tsara ficewarsu zuwa jam’iyyar APC.
Jigajigan na PDP, wadanda suka hada da tsofin kwamishinoni, tsofin yan majalisun jiha dana tarayya, tsofin shugabannin kananan hukumomi da dai sauransu, sun karaya da yanda haske da tauraron jam’iyyar PDP ke kara dishashewa a jihar.
Ranar wanka a ka ce ba a boyon cibi, babbar matsalar jam’iyar PDP a jihar Gombe itace yayanta, musamman ma wadanda ya kamata a ce su za su jagoranceta zuwa nasara a zaben 2023, amma saba nin hakanne ke faruwa a yanzu.
Irin gaban kai da tukin ganganci da nuna warayya da dan takaran PDPn na kujerar Gwamna a jihar, Muhammad Jibrin Dan Barde yake nunawa su ne babbar silar koma baya da dishashewa da tauraron jam’iyyarke cigabada yi a jihar Gombe.
Tun bayan da ya samu nasara a zaben fidda gwani, Dan Barde ya nesanta kansa daga ‘ya’yan jam’iyyar da shugabanninta, sai wanda yaga dama yake kulawa.
Zuwa yanzu, babu wani cikin makusantan mutum biyar da sukayi takara tare da Dan Barde da Dan Barden yake sakashi cikin harkokinsa. Ya takaita harkokin nasa ga iya mutanensa da suke tare tun kafun zaben fidda gwanin.
Bugu da kari, har zuwa yanzu babu jituwa tsakanin dan takaran Gwamna na Jam’iyyar PDPn, da sauran ‘yan takaran dake takaran kujerun majalisun tarayya dana jiha, wanda a yanzu haka da yawannsu basa ma batunsa awajen neman alfarman kuri’a da suke nema wajen al’ummar su.
Kashi sama da tamanin cikin dari na wadanda su ka yi aiki da tsohon gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ba sa cikin tafiyar Dan Barde. Wannan ba zai rasa nasaba da irin suka da adawa da Dan Barden ya yiwa Dankwambo lokacin mulkinsa ba, yayin da Dan Barden ke jam’iyar APC a wancan lokaci ba.
Iyalan wani mamaci sun bada gudummawar injin wankin ƙoda ga asibitin Aminu Kano
Alamu sun nuna cewa Dan Barde bai son baiwa duk wani da ya yi alaka da gwamnatin Dankwambo damar shiga jihinsa
A yanzu Dan Barden ya riga ya ware wadanda zaiyi aiki dasu da wadanda bazaiyi aiki dasu ba cikin mambobi da shugabannin jam’iyyar.
Wannan hali na nuna warayya da Dan Barde yake nunawa, da kuma zargin kasancewarsa mutum mai matukar nuna izza da jiji dakai, yasa mambobin jam’iyyarmu suke kauracewa shiga sabgarsa.
Da wannan tarin matsaloli da rashin rungumar dukkan ‘yayan jam’iyyar za mu ce jam’iyyar ba ta kama hanyar neman nasara a zaben sheka ta 2023 dafe ba.