Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar kano tace zata gabatar da kasafin kudin shekara ta 2023 ga Majalisar dokokin jihar kano a wata Mai kamawa na October.
Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin taron majalisar zartarwa ta jihar kano wadda ake gabatarwa mako-mako a Gidan gwamnatin Kano.
Gwamnan Ganduje yace gwamnatin kano, tana kokarin taga tabi Sabuwar dokar kasafin kudi, wadda tace dole ne bangaren zartarwa ya gabatarwa majalisar dokoki kasafi kudi akan lokaci, Kuma ita ma majalisar ta kammala aikin ta akan lokaci domin fara aiwatar da sabon kasafin kudin a ranar daya ga watan sabuwar shekara.
Yace ya kamata ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kammala Aikin ta akan lokaci, domin gwamnati ta gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a watan gobe.
Gwamna Ganduje ya kuma bukaci sabbin kwamishinonin da aka rantsar, wanda kuma suka fara halartar taron majalisar zartarwar a wannan makon, da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun bada gudunmawa domin gwamnati ta kammala dukkanin aiyukan da ta ke gudanar a Kano kafin karewar Wa’adin gwamnati.
Ya kuma bukace su da yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar APC ta Sami nasara a zabukan shekara ta 2023 dake tafe