Hukumar Kula da kafafen yada labarai ta hana sa wakar ” Warr ” ta Ado Gwanja a Radio da Tv

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ta haramta sanya wakar Ado Gwanja ta WARR a gidajen Radiyo da Talabijin na kasar nan.

Hakan na dauke ne cikin wata Sanarwa da hukumar ta fitar mai kwanan watan 06 ga watan Satumba 2022.

Kadaura24 ta rawaito wakar ” Warr ” na daya daga cikin manyan wakokin mawakin wadanda suka shahara a wannan musamman a wajen mata.

Sanarwar da tace an dakatar da sanya wakar ne a radio da Talabijin Saboda wasu kalamai da yake yi a cikin baitocin wakar ta Warr wadanda suka Saba da dokokin hukumar da Kuma al’adar Hausawa.

Wasu baitoci cikin wakar Warr wadanda suka hadar da : 

” ….kafin a San mu ai mun ci kasahin uban mu…

“….zani zo bari insha fa hoda, ko kin zo da hodar ki uban ki zan ci warr…

“… Kowa yace zai hana ni uban sa zan ci..

Sanarwar tace wadannan baitoci da suke cikin wakar ta Warr sun sabawa sashin na 3, 18, 2c  na hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC.

 

Sabawa wannan umarni na hukumar NBC ga kafafen yada labarai na Radio da Talabijin zai iya sanyawa a hukunta kafar yada labaran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iya shugabanci: Gwamnan Kano ya sake karbar lambar yabo

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Jaridar Vanguard ta Karrama Gwamnan Jihar...

Kisan Gilla: Muhimman abubuwan da Gwamnatin Kano ta gabatar wa gwamnatin Edo

Hukumomi a jihar Kano, sun yi ƙarin haske game...

Yadda za mu koyawa Matasa 5000 Noman zamani – Shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are

Daga Rahama Umar Kwaru   Shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama'are Engr...

Atiku, El-Rufai, Tambuwal Sun Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa – Buhari

Daga Rahama Umar Kwaru   A ranar Juma’a Nan 11 ga...