Rt. Hon. Yan’shana ya fara aiki a matsayin sabon kwamishinan Ilimi na jihar Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Sabon kwamishinan ilimi na jihar Kano Rt. Hon. Ya’u Abdullahi Yan’shana ya yi alkawarin yin aiki tukuru wajen ganin an cimma manufofin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na bunkasa harkar ilimi a jihar kano.

 

Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa ta farko da ma’aikatan gudanarwar na ma’aikatar bayan shigarsa ofis a jiya Litinin.

 

Ya ce ma’aikatar ilimi tana daya daga cikin manyan ma’aikatu a jihar da ke da ayyuka masu muhimmanci, don haka dole ne kowa ya tashi tsaye domin tabbatar da gudanar da ayyuka masu inganci wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Talla

 

Yan shana ya yi nuni da cewa, a matsayin ma’aikatar ilimi wadda aka dora mata alhakin bayar da ingantacciyar tarbiyya da ilimin yara tun suna yara har su girma, yace ya kamata ma’aikatan ma’aikatar da sauran masu ruwa da tsaki su dauki aikin da muhimmanci Kuma su rike shi bisa gaskiya da rikon amana.

 

Rt. Hon. Yan’shana wanda ya bukaci ma’aikatan gudanarwa da su rika sanya Kano da jama’a a kodayaushe a gaba, ya jaddada bukatar yin aiki tukuru, sadaukar da kai domin cimma burin samar da ma’aikatar.

Talla

 

A yayin da yake neman goyon baya da hadin kan ma’aikatan ma’aikatar, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tukuru da kuma yi iya gwargwadon ikonsa a tsawon lokacin da zai yi a matsayin Kwamishinan Ilimi a ma’aikatar.

 

Ya kuma ba da tabbacin yin aiki da kowa Kuma a bude tare da baiwa kowa damar gudanar da aikinsa kamar yadda ya rataya a wuyansa.

 

Sai dai ya yi nuni da cewa ya yanke shawarar fara ayyukansa ne da ganawa da ma’aikata da nufin sanin ma’aikatun da suke karkashin ma’aikatar da ayyukansu da Kuma kalubalen da suke fuskanta, ta yadda zai iya samar da sauye-sauyen da za a iya amfani da su don ciyar da ma’aikatar gaba.

 

Tun da farko, a jawabinta na maraba yayin taron, Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Lauratu Ado Diso ta bada tabbacin bada goyon baya da hadin kan daukacin ma’aikatan ma’aikatar da ma na sauran sassan ma’aikatar ga sabon kwamishinan don ya samu nasarar aikin da aka dora masa .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...

Rabon Jakai: Faizu Alfindiki ya aikawa Sanusi Bature budaddiyar wasika

Zuwa ga: DG. Sunusi Bature Dawakin Tofa Daraktan Yada Labarai, Gwamnatin...

Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili

Daga Isa Ahmad Getso   Sarkin Kano na 15 Aminu Ado...