Daga Kabiru Muhammad Getso
A yau ne Sabon Kwamishinan ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta jihar kano Alhaji Ibrahim Dan azumi Gwarzo ya shiga Ofis da domin fara aiki ranar Litinin.
Da yake ganawa da manema Labarai Hon Dan Azumi Gwarzo ya bayyana cewa Babban abinda yake bukata ga al’ummar Jihar kano Addu’a domin samun damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Yace Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Ma’aikatace da take bukatar bi a sannu tare da sanin makamar aiki, domin bin ka’idojin ayyuka don anfanuwar al’ummar jihar Kano.

Ya Yabawa Gwaman Jihar kano bisa wannan dama da ya bashi ta shugabantar ma’aikatar, inda ya tabbatar da yin aiki tukuru domin anfanin al’ummar jihar kano, musamman ganin yadda yake da kwarewa a fannin.

A shekarun baya dai ya taba rike kwamishinan ma’aikatar kudi kuma ya kammala lafiya ba tare da samun wasu kalubale ba.
A makon da yagaba ne Gwamna Ganduje ya Rantsar da sabbin kwamishinoni guda 11 wadanda ya umarcesu da su fara aiki gadan-gadan a wannan rana ta litinin.