Daga Rahama Umar Kwaru
Birnin Kano ya cika da Baki daga sassa daban daban na ciki da wajen kasar nan domin shaida Daurin Auren ‘yar Sarkin Kano Rukayya Aminu Ado Bayero.
Da yake adduar Daurin Auren babban limamin Kano Professor Muhammad Sani Zaharadeen ya ce Ango Amir UK Umar ya biya Sadakin Amaryarsa Rukayya Aminu Bayero naira Dubu Dari biyu.

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya Zama waliyin Rukayya Aminu Ado Bayero, Wanda shi ne ya bayar da Aurenta ga Amir UK Kibiya.
Babban sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 cewa, Sarakuna daga sassan kasarnan da Gwamnoni da manyan Masu kudi da Yan kasuwa na cikin kasar nan da wajenta sun halarci taron Daurin Auren.