Daga Abubakar Sadeeq Na kowa
Gidauniyar Aliko Dangote take aikin masara da Abinchi mai gina jiki ga yara mai suna Aliko Dangote Foundation Integrated Nutrition Project (ADFIN) ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin jihar Kano domin duba matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar.
Taron ya gudana ne a sashin ECA na asibitin Abdullahi Wase da ke Kano a ranar Laraba.
Da take jawabi gabanin rattaba hannu kan yarjejeniyar a hukumance, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Yousufou ta ce gidauniyar ta damu matuka da yawaitar rashin abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin yara a jihar.
A cewarta, gidauniyar ta riga ta tallafa wa shirin ciyarwa na Hajiya Mariya Dantata, wanda take raba abinci ga kusan mutane 30,000 a kullum.
Ta kuma bayyana cewa wani bangare na kudirin gidauniyar na duba akan matsalar rashin abinci mai gina jiki shi ne rabon biredi ga mutane 20,000 a kullum a Kano, da kuma mutane 10,000 a Legas.
Ta bayyana cewa ya na cikin yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kai alkawarin sama da Naira miliyan 50 don siyo kayan Abinci da za’a yi amfani da shi wajen kula da yara masu fama da matsananciyar tamowa, a jihar kano .
“Babban abin da Gidauniyar Aliko Dangote ta mayar da hankali a kai shi ne abinci mai gina jiki wanda ya kunshi ayyukan da suka shafi lafiya, ilimi da inganta Rayuwar al’umma” .
“A kan haka, a yanzu muna zuba jarin da ba a taba yin irinsa ba don inganta abinci mai gina jiki a kasarmu.
“Muna bukatar kawo karshen wannan annoba ta rashin abinci mai gina jiki kuma mun sanya hannu kan wannan yarjejeniya don ta kai mu ga cimma burinmu.
“Duk da haka muna rokon sauran abokan hulda da kwararru da su hada hannu da mu don cimma matsaya mai dorewa,” in ji Yusufu.
A nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya yabawa hamshakin dan kasuwar, Aliko Dangote da gidauniyar sa bisa yadda suke bada gudunmawa mai tsoka domin inganta lafiya da jin dadin al’ummar jihar kano.
Dokta Tsanyawa ya baiwa Gidauniyar tabbacin yin duk mai yiwuwa don bayar da hadin kai don cimma burin da ake da shi na sauya kididdigar Masu fama da rashin samun abinci mai gina jiki a jihar.