Daga Ibrahim Sani Gama
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa da hukumar kashe gobara ta jihar kano da sauran jamian yansanda da alumma da dama na cigaba da kokarin tono mutanen da gini Mai hawa biyu ya ruftawa a kasuwar wayar hannu ta Berui dake Kano.
Al’umma da dama a cikin kasuwar suna ta alakanta abin da cewa son rai ne daga cikin wasu shugabancin kungiyar kasuwar ya haifar da hakan.
A wata ganawa da yayi da manema labarai jami’in hulda da jami’a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Yusuf yace har yanzu ba’a kiyasce yawan mutanen da ginin ya danne ba, amma ana cigaba da ceto mutane tare da mikasu Asibiti domin samun kulawar likitoci.
Wakilin Kadaura24 wanda yanzu haka yake wajen da lamarin ya faru yace akan idonsa an sami nasarar ceto mutane 7 daga ciki da ransu.
NIMET ta yi hasashen samun ruwan sama mai karfi a jihohi 5 na arewacin Najeriya
Wakilin na mu yace yana ta kokarin jin ta bakin shugabancin kungiyar kasuwar amma hakan ya ci tura.
Zamu cigaba da Kawo muku halin da ake ciki.