Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya zata ciyo bashin Naira Tiriliyan 11a shekara ta 2023 – Ministar Kudi

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Ministar Kudi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin naira Tiriliyan 11 tare da sayar da wasu manyan kadarorinta domin samun kudin da za a cike gibin kasafin kudin shekarar 2023.

 

Ministar tace ana sa ran gibin kasafin kudin kasar zai zarta naira tiriliyan 12.42, idan har akaci gaba ta bayar da tallafin man Fetur a gaba dayan shekarar 2023.

Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ta hallara gaban kwamitin kudi na majalisar wakilai domin gabatar da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa’adi na shekarar 2023 zuwa 2025.

Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da a ka yi kan hanyoyin ruwa

Yayin da take bayanin hanyoyin biyu da za a cike gibin ga kwamitin, Ministar ta ce hanya ta farko ta hadar da ci gaba da biyan tallafin man fetur har karewar  shekarar 2023

Ta ce hanya ta farko an yi hasashen cewa gibin zai kai naira Tiriliyan 12.41 a 2023, idan haka bi wannan hanya gwamnati za ta kashe tiriliyan shida kan tallafin man fetur.

 

Ambaliyar ruwa: Atiku ya bada tallafin Naira Miliyan 50 ga yan kasuwar K/ Kwari

Hanya ta biyu kuma ta kunshi ci gaba da biyan tallafi zuwa watan Yunin 2023, a wannan kuma gibin zai kai naira Tiriliyan 11.30, inda ake hasashen tallafin da za a biya zai kai naira tiriyan 3.3.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...