Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa al’ummar jihar Kano musamman wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a wannan lokaci da ake ta samun ambaliyar ruwa a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Kuma ya aikowa kadaura24, sanarwar tace Sarkin ya bayyana alhininsa game da ambaliyar ruwa da aka gani a wasu sassan jihar.
Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da a ka yi kan hanyoyin ruwa
Sarkin ya yi kira ga al’umma da su guji zubar da shara a hanyoyin ruwa domin kaucewa afkuwar lamarin nan gaba.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya jaddada bukatar malamai su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai domin magance matsalolin ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rasa matsuguni da asarar dukiyoyi.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a wurare da daban-daban a jihar Kano an sami ambaliyar ruwa data jawo asarar miliyoyin kudi da Kuma rasa rayuka .