2023: Duk ƙuri’un da Buhari ke samu a Arewa sun zama na Kwankwaso, in ji Kofa 

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Dan takakar majalisar wakilai, mai wakiltar Kiru da Bebeji na Jam’iyar NNPO a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce Sanata Rabi’u Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, yanzu shi ne zai gaji ɗaukacin ƙuri’un da ƴan arewa ke kaɗa wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓe.

 

Abdulmumini Jibrin ya bayyana haka ne a jiya Juma’a, a wata hira da gidan talabijin na Channels.

Kishi: Wata Mata ta Kashe Tsohon Mijinta a Jihar Kebbi

 

Idan dai za a iya tunawa, an yi ta raɗe-radin cewa Kwankwaso zai nemi magoya bayansa su zaɓi Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.

Talla
Talla

 

Da yake mayar da martani kan wannan batu, Jibrin, wanda shi ne kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na Kwankwaso, ya ce tsohon gwamnan baya tunanin haɗewa da APC.

 

2023: Zamu Haɗawa Gawuna da Garo Kwararru Miliyan Daya don su Sami Nasarar Zaben Gwamnan Kano – GAPON

Ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da zai samu kuri’u fiye da Kwankwaso a yankin Arewacin kasar nan.

 

“Mun karyata wadannan karairayin da ake ta yaɗa wa akai-akai. Wani yunƙuri ne na ba wa jama’a ra’ayi da bai dace ba don wata ƙungiya ko biyu su sami damar ɗaga matsayinsu a bainar jama’a,” inji shi.

 

“Kwankwaso gogaggen ɗan siyasa ne. Mu da gaske mu ke. Ba dan wani mu ke takarar nan ba kuma na sha fadar haka a lokuta da dama.

 

“Sabo da haka ina kira ga al’umma da su yi watsi da wannan farfaganda cewa Kwankwaso na yi wa Asiwaju aiki ne ko za mu haɗe da APC .

 

“Ya za ai ma haka ta yiwu. Mutumin da shi ne ke da ikon Arewa gaba ɗaya. Mutumin da shi zai gaji ƙuri’u miliyan 12 na Buhari a Arewa. Kwankwaso ya fi ko wanne ɗan takara farin jini da masoya da mabiya a halin yanzu,” in ji Kofa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...