Daga Rukayya Abdullahi Maida
Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP Engr. Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da (Abba Gida Gida) ya roƙi Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau da mutanensa da suyi haƙuri su zauna a jam’iyyar NNPP don kawar da gwamnatin jam’iyyar APC a Kano.
Abba Kabir yayi wannan jawabi ne a wani zama da yayi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar don mayar da martani akan wasu kalamai da Malam Ibrahim Shekarau yayi na zargin rashin adalci da akayi masa a yayin musayar sunayen ƴan takara.
“Bama fatan gidan siyasar Shekarau su fita daga jam’iyyar mu, muna fatan zasu fahimci halin da al’ummar Kano ke ciki don ceto su daga wannan hali da suke ciki”. Inji Abba Kabir Yusuf
Idan dai ba a manta ba, an ja zare tsakanin gidan siyasar Munduɓawa da Kwankwasiyya, inda aka fara yada magana tsakani.
jaridar Siyasarmu ta rawaito anci gaba da raɗe raɗin cewar Malam Ibrahim Shekarau da tawagarsa ƴan shura na iya ficewa daga NNPP zuwa PDP bisa tayin da ɗan takarar shugabancin Kasar nan a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar yayi masa na bashi Coodinatansa na shiyyar arewa maso yamma.