Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da rufe hedikwatar jam’iyyar da gwamnatin Jihar Borno ta yi.
A cikin wata sanarwa da Kwankwason ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.
Hukumar Kula da ‘Yan sandan Najeriya za ta tafi yajin aikin sai baba ta gani
Ya kara da cewa suna yin duk abin da ya kamata wajen ganin an bude sakatariyar jam’iyyar da aka garkame.
Gwamnatin Buhari tafi kowacce gwamnati a Nigeria yiwa Kano Aiyukan raya Kasa – Ganduje
Lamarin na faruwa ne yayin da Kwankwason ke shirin zuwa jihar a ƙarshen wannan makon.
Kadaura24 ta rawaito idan ba’a manta ba a yau alhamis an wayi gari da gani tarin jami’an tsaro a helkwatar jam’iyyar ta NNPP dake a Maiduguri babban birnin jihar Borno