Daga Rahama Umar Kwaru
Majalisar hadin guiwa ta Hukumar Kula da ‘Yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwar tafiya yajin aikin na sai baba ta gani, saboda saba yarjejeniyar da aka cimma.
Shugaban kungiyar ma’aikatan reshen hukumar ‘yan sandan kasar, Adoyi Adoyi, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar.
2023: A shirye muke mu yi kawance da wasu jam’iyyun – NNPP
Kungiyar ta bayyana cewa yajin aikin zai fara aiki ne daga ranar Litinin 29 ga watan Agusta, 2022.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin shugaban hukumar Musiliu Smith da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Baba, kan daukar sabbin ma’aikata, musamman karin girma ga kuratan ‘yan sanda.
Gwamnatin Buhari tafi kowacce gwamnati a Nigeria yiwa Kano Aiyukan raya Kasa – Ganduje
Shugaban kungiyar ya lura da cewa, babban sufeton ‘yan sandan da sauran shugabannin ‘yan sanda tare da shugaban hukumar, sun yi watsi da dokar daukar sabbin ma’aikata.