Daga Abdulrashid B Imam
Wani dan siyasa a Kano, Nasiru Koguna, ya yi ikirarin cewa har yanzu shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, a jihar Kano, ba Sha’aban Sharada ba.
A wata wasika da ya aike wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Koguna, ta hannun lauyansa Farfesa Nasiru Aliyu, SAN, ya ce wakilan jam’iyyar shi suka zaba a matsayin dan takarar ADP.
Ya kara da cewa shi da kansa bai rubuta wa hukumar zabe ta INEC cewa ya janyewa Wani ba kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.
Yanzu-Yanzu: Ganduje zai Samar da karin jami’o’i guda biyu a kano
“A madadin HON. NASIRU HASSAN KOGUNA Dan jam’iyyar ADP tun da dadewa, shi ya bukaci mu rubuta muku wannan wasika a madadinsa ,” kamar yadda wasikar ta bayyana.
“Za ku iya tunawa, abokin huldar mu wato dan takarar jam’iyyar ADP a zaben gwamnan jihar Kano a babban zaben 2023 mai zuwa shi ne wanda jam’iyyar ta turawa hukumarku sunansa .
Kisan Sheikh Aisami: Yan Sanda sun chanchanci yabo – Mal. Dauda Lokon Makera
“Takardar mu ta bayyana cewa, wanda muke wakilta ya shiga zaben fidda gwani kuna wakilan jam’iyyar shi suka tabbatar a matsayin Dan takarar gwamna wanda ya sami goyon bayan 748 da suka cancanci zabar dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.”
Wasikar ta kara bayyana yadda shugaban jam’iyyar na kasa ya shirya yadda aka sauya sunansa ba tare da bin ka’ida ba kamar yadda doka ta tanada.