Gwamnatin Buhari tafi kowacce gwamnati a Nigeria yiwa Kano Aiyukan raya Kasa – Ganduje

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar kano ta yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda da managartan aiyukan tituna da gwamnatin sa ta gudanar a jihar nan don cigaban harkokin kasuwanci a jihar.

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya yi yabon lokaci da yake jawabin a taron kwamishinonin aiyuka na jihohin wadanda suka hadu a wani taro da aka Saba yi duk shekara, domin tattauna yadda za’a samar da kuma karasa aiyukan da gwamnatin tarayya take gudanarwa a jihohin su.
Gwamna Ganduje yace gwamnatin tarayya tarayya ta gudanar da aiyukan hanyoyin Masu tarin yawa wadanda idan an kammala su zasu taimaka wajen inganta tattalin arzikin jihar kano kasancewar kanon cibiyar kasuwanci a arewacin Nigeria dama wasu kasashen yammacin Africa.
Yace akwai aiyuka da dama da gwamnatocin baya suka fara Amma suka watsar, Amma da zuwan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yanzu haka wasu daga cikin aiyukan sun kusa kammaluwa.
Ganduje ya kara da cewa e yanzu haka gwamnatin tarayya tana gudanar da aiyukan hanyoyi a duk wata hanya da ta haɗa Kano da wasu jihohin, kamar kano zuwa Kaduna da Kano zuwa Maiduguri da kano zuwa Katsina da Kano zuwa Hadeja da Kuma kano zuwa Daura.
Da yake nasa jawabin Ministan Ma’aikatar aiyuka da gidaje ta kasa Babatunde Raji Fashola ya ce gwamnatin Buhari tana gudanar da aiyukan ne a kano da sauran jihohin kasar nan domin inganta harkokin sufi da Kuma Samar da aiyukan yi ga al’umma.
 Ministan yayi alkawarin gwamnatin tarayya Zata kammala dukkanin aiyukan da ta dauko kafin karewar Wa’adin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a shekara ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...