2023: A shirye muke mu yi kawance da wasu jam’iyyun – NNPP

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufa’i Alkali, a ranar Larabar da ta gabata ya ce jam’iyyar a shirye take ta hada kai da wata jam’iyyar kafin zaben 2023 mai zuwa.

 Malam Alkali, mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa ne ya bayyana hakan a Legas a wani taron manema labarai.
 A cewarsa, jam’iyyar ba ta kyamar tattaunawa da wasu jam’iyyun don gina kasar nan.
 “ kowacce jam’iyya tana da damar zuwa mu tattuna Amma Jam’iyyun da ke son tattaunawa dole ne mu bayyana ra’ayoyinmu kan makomar kasar nan.
 “Dukkan jam’iyyu daidai suke a doka.
 “Muna magana ne game da makomar Najeriya,” in ji Mista Alkali, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa.
 Premium Times ta rawaito  ya kuma yi tir da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a Najeriya, yana mai cewa bai kamata mutane su zo a tattauna da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya janye burinsa na karar Shugaban kasa ba.
 Tattaunawar kawance tsakanin jam’iyyun NNPP da Labour ta tsawon makonni ta kasa haifar da sakamakon da ya sa ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun biyu – Kwankwaso da Peter Obi .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...