- Daga Buhari Ali Abdullahi
Wani lauyan Mai suna Barr. Badamasi Sulaiman Gandu yayi barazanar maka hukumar hisba ta jihar kano a gaban kotu matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin matan nan wato Ado Isa Gwanja daga fitar da wata Sabuwar waka da yayi Mai suan “Asoso”.
Da yake zantawa da wakilin Kadaura24 asafiyar yau Barista Badamasi Silaiman Gandu yace tuni ya aike da takardun gargadi na kwana uku ga hukumomin HISBA da hukumar Shari’a ta jihar kano domin su gaggauta dakatar da mawaki Ado gwanja daga fitar da sabuwar wakarsa mai suna “Asosa”.
Barr. Gandu Wanda ya zargi mawakin da yin amfani da kalaman da basu daceba acikin wakokinsa, yace barin irin wadannan wakokin a cikin al’umma zai kawo cikas wajen tarbiyyar yara masu tasowa.
Yanzu-Yanzu: Ganduje zai Samar da karin jami’o’i guda biyu a kano
Lauyan yace kamata ya yi gwamnatin jihar Kano ta dauki mawakin aiki a karkashin hukumar HISBA domin yin amfani da hikimarsa wajen fadakar da al’umma sabanin yadda yake amfani da hikimar ta wata hanya daban.
A karshe lauyan yayi barazanar maka hukumar HISBA agaban kotu matukar ta haura kwana uku bata dakatar da mawaki ado gwanjaba daga fitar da sabuwar wakar ba Mai suna “Asosa “