Kisan Sheikh Aisami: Yan Sanda sun chanchanci yabo – Mal. Dauda Lokon Makera

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wani Malamin addinin musulunci a Kano, Shaikh Muhd Dauda Lokon Makera, ya yabawa rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa yadda ta kama wadanda ake zargi da kashe Shaikh Goni Aisami a jihar Yobe cikin gaggawa.

 Malamin addinin Musuluncin ya kuma ce, umarnin da aka baiwa sojoji na su binciki zargin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, shima abin a yaba ne.
 “Mun Sami nutsuwa  a yanzu saboda muna da tabbacin hukuma za ta yi abin da ya dace kan wadanda ake zargi da kisan kai, muna son a yi wa Shaikh Aisami da iyalansa da dalibansa adalci.
 Shaikh Dauda Lokon Makera ya kuma jinjinawa jajircewar al’ummar jihar Yobe da ma musulmi baki daya, saboda kasancewarsu masu bin doka da oda a lokacin da lamarin ya faru, yana mai kira ga hukumomi da su tabbatar da Adalcin da zai gamsar da kowa da kowa.
 Malamin ya kuma koka da cewa har zuwa lokacin da ya sani, babu wata kungiya ta Kirista da ta yi yabo ko tausaya wa al’ummar Musulmi kan lamarin.
 Ya kuma yi kira ga MusulminbNajeriya baki daya da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya da kuma zama masu bin doka da oda domin tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...