Daga Abdulrashid B Imam
A yau Litinin ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance tare da amincewa da naɗin kwamishinoni guda tara da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa.
Tun da fari, hugaban majalisar, Hamisu Ibrahim-Chidari ya sanar da karɓar wasiƙar Ganduje, na neman karin kwamishina ɗaya mai suna Dakta Aminu Ibrahim-Tsanyawa, wanda majalisar za ta tantance tare da tabbatar da shi.
Rundunar yan sanda ta turo sabon Kwamishinan yan sanda jihar kano
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 15 ga watan Agusta ne kakakin majalisar ya sanar da karbar wasikar da Gwamna Ganduje ya rubuta domin tantancewa tare da tabbatar da wasu daga cikin kwamishinonin da aka nada.
Hakan ya biyo bayan murabus din da wasu ‘yan majalisar zartaswar jihar suka yi na tsayawa takara a babban zaben 2023.
Sabbin kwamishinonin sun hada da: Ibrahim Dan’azumi, Abdulhalim Abdullahi, Lamin Sani-Zawiyya, Ya’u Abdullahi-Yan’shana, Garba Yusuf Abubakar da Dr Yusuf Jibirin.
Sauran sun hada da Adamu Fanda, Saleh Kausami, da Dr Ali Burum-Burum.
Ibrahim-Chidari ya ce an aika da wasikar gayyata ga Ibrahim-Tsanyawa da ya bayyana a gaban majalisar a ranar Talata, domin tantancewa.
An tantance sunayen mutane tara kuma ƴan majalisar sun tattauna kan tantancewar wanda hakan ya sa aka tabbatar da kwamishinonin.