Daga Rahama Umar Kwaru
Dan takarar dan majalisar wakilai a kananan Hukumomin kura, Madobi da Garun Malam a tutar jam’iyyar APC Hon Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso na cigaba da karbar ‘ya ‘yan Jam’iyyar NNPP zuwa APC a yankin.
Hon. Rabi’u Abdulmalik Juda da Alhaji Bala Kubaraci Garkuwa na daga cikin wadanda suka ajiye tafiyar jam’iyyar NNPP kwankwasiyya suka Kuma rungumi tafiyar jam’iyyar APC.
Hon. Bala Kubaraci Garkuwa ya taba zama Mataimaki na Musamman ga Dr Rabiu Musa Kwankwaso Dan Takarar Shugaban Kasa a NNPP Mai kula da jIhar Kaduna, yace lokaci yayi da zasu marawa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da Dr Musa Ilyasu baya don samun nasara jam’iyyar APC musamman a yankin Kura Madobi Garun Malam dama Kano baki daya.
Ganduje zai nada matashi mai shekaru 33 kwamishina a kano, waye shi ?
“Ba’a taba mutumin da naso a Siyasance ba kamar Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, nayi tallan Kwankwaso da kwankwasiyya a Kano ko Nigeria kadai ba har kasar Ghana naje nayi tallan Kwankwaso, to tunda ka ga bar tafiyar ai kasan akwai dalilai Masu karfi da nake da su”. Inji Bala kubaraci
Da yake zantawa da kadaura24 Dr Musa Ilyasu Kwankwaso wanda shi ne sarkin yakin Masarautar karaye ya yaba da yadda matasan jam’iyyar NNPP suke ajiye tafiyar suna rungumar tafiyar APC.
“Babu Shakka sun yi kyan Kai da suka ajiye tafiyar da ake wahalar da su, suka kuma dawo jam’iyyar APC don su bada tasu gudunmawar don ganin APC ta Sami nasara a zabukan shekara ta 2023”. Inji Musa Iliyasu

duk a jiya asabar Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya jagoranci guda cikin sabbin yan APC wato Hon Rabi’u Abdulmalik Juda wajen kai ziyara ga dan takarar mataimakin gwamnan kano Hon. Murtala Sule Garo.
Shura ta baiwa Shekarau sharudda 5 na sauya sheka zuwa PDP
Yayin ziyarar sun tattauna muhimman batutuwan da zasu kawowa jam’iyyar APC Nasara a zabukan shekara ta 2023.
Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso (Sarkin Yakin Karaye) dan takarar majalisar tarayya, shi ne ya jagorancin Tawagar mutanan Kura da garum Malam, wajen kai Wannan ziyara, yan tawagar sun hadar da Hon. Mustapha Abdullahi Kura da Hon.Rabi’u Abdulmalik Juda Sabon dan jam’iyyar APC. da dai sauransu.