Daga Auwal Alhassan Kademi
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ba tattaunawar siyasa suka yi da ɗan takarar shugabanci kasa na APC ba, Bola Ahmed Tinubu.
Obasanjo ya gargadi magoya bayan Bola Tinubu kan yaɗa cewa ya marawa takarar Tinubu baya a ganawar sirri da suka yi a gidansa da ke Abeokuta a ranar Laraba.
Musa Iliyasu Kwankwaso na cigaba da daka wawaso a cikin NNPP ta Kura Madobi da Garun Malam
Ya ce yaɗa irin wadannan labarai marasa tushe na lahani ga ‘yan siyasa irinsu Tinubu.
A wata sanarwa da maitaimaka ma sa na musamman ya fitar, kehinde Akinyemi, na ambato Obasanjo na cewa ganawarsa da Tinubu ta ‘yan uwantaka ce ba siyasa ba.
Ganduje zai nada matashi mai shekaru 33 kwamishina a kano, waye shi ?
Wannan na zuwa ne bayan kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a wani taro na APC a Lagos ya na mai cewa ganawar Obasanjo da Tinubu alamar nasara ce garesu a zaben 2023.
Tsohon shugaba Obasanjo dai ya sake jadada cewa shi uba ne ga duk ‘yan Najeriya da matasa da ke cikin matsi.