Kungiyar Kanam Media Hub ta horas da mata yan jaridu dabarun aiki a Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar Kanam media Hub,  mamallaka kamed development TV sun shirya taron karawa juna sani na yini guda a ranar Alhamis don bada horo ga yan jarida mata masu tasowa a radio don su inganta aikinsu Kamar yadda ya kamata.

 

Da take jawabi a wajen taron shugabar kungiyar Amb. Khadija Ishaq Bawas tace sun shirya taron ne ga yan jaridu mata dake kano don zaburar dasu su  sami karsashin yin aikin, da Kuma samun kwarewa a wasu fannonin da zasu iya aiwatar da aikin koda basa gidan Radio.

 

Tace a bayan sun bayar da horonne ga mata masu aikin a gidajen talabijin, bayan kuma sun yi dogon nazari sai suka ga ya dace a horar da mata dake aiki a gidajen Radio.

Talla
Talla

 

“Wannan tasa a wannan karon mukafi ?mai da hankali ga yan radio ta hanyar koya musu hanyoyin dogaro da kai da Kuma nuna musu hanyoyin koya ayyuka kala daban-daban koda da wayar hannu ne ba tare da sun ta’allaka a iya aikin radio kadai ba”. Inji Bawas

 

Bawas ta Kara da cewa kungiyarsu bata tsaya anan ba, ko a baya tayi taro makamancin wannan, game da binciken kwakwaf a aikin jarida, da kuma cin zarafin mata da sauransu.

 “A baya mun kirkiri wani ofishi na wayar da kai, inda muka ziyarci wani kauye dake Karamar hukumar wudil mai suna Utai, inda muka wayar da kan maza da mata game da illar cin zarafi ‘ya’ya mata da wayar da kansu kan yadda zasu kula da kansu yayin al’ada”.

 

“Ya yayin da muka je garin mun raba audigar mata, da kuma wayar da kan maza yadda zasu dinga tausayawa mata sannan Suma mazan an raba musu sabulai da wayoyin hannu guda 10 domin su rika bada rahoton duk abun da basu yarda dashi ba ga jami’an Rundunar yan sanda dake yakin don inganta tsaron rayuka da dukiyoyin su”.

 

Hon. Justice Yahya Muhammad kamed kadi ne daga kotun daukaka Kara dake jihar Filatu, Wanda kuma shi ne babban Bako a wurin taron,  cewa yayi zai so mata yan jarida su Kara kwazo da hubbasa a aikin, sakamakon aiki ne mai mahimmanci wurin taimakawa a gyara lamurra tsakanin jama’a.

Yace kasancewar ta hanyar Yan jarida ne ake shawo kan Abubuwa daban- daban da matsalolin dake damun Al’umma, akwai bukatar wadanda suke aikin su yi shi bisa kwarewa da sanin makama domin kwalliya ta cigaba da biyan kudin sabulu.

 

A Karshe ya yi kira ga mata Yan jarida masu tasowa dasu kara kaimi, kana suyi aiki da gaskiya da Amana, kasancewar aikin na bukatar wadannan Abubuwa guda biyu, domin da gaskiya da Amana ne zasu yada labarai da Kuma taka  tsantsan a sha’anin aikin nasu.

 

Taron wanda ya gudana da shi a nan kano, ya samu halartar mata matasa Yan jarida daga kafafen yada labarai daban-daban musamman ma’aikatan gidajen radio, wanda kungiyar ta Basu takardar shedar samun horon na kwana guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...